ha_tn/jos/07/14.md

1.4 KiB

Mahaɗin Zance:

Yahweh ya cigaba da gaya wa Yoshuwa abinda zai gaya wa mutanen.

dole ku taru bisa ga kabilarku

Akwai kabilu goma sha biyu da suka kumshi mutanen Isra'ila. Jimlar nan "bisa ga kabilarku" na nufin "kowace kabila". AT: "dole kowace kabilarku su taru su gabatar da kansu ga Yahweh" (Duba: figs2_idiom)

Kabilar da Yahweh ya zaɓa

Shugabannin Isra'ila za su jefa kuri'a, ta yin haka ne, za su san ko wanne kabila ne Yahweh ya zaɓa. AT: "Kabilar da Yahweh ya zaɓa ta wurin kuri'a" ko kuma "Kabilar da Yahweh ya zaɓa idan mun jefa kuri'a"

Kabilar da Yahweh ya zaɓa za ta matso iyali - iyali

Kabilar ta kumshi iyalai AT: "Daga kabilar da Yahweh ya zaɓa, kowace iyali za ta matso kusa" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-idiom)

Iyalin da Yahweh ya zaɓa dole su matso gida - gida

Iyalin sun kumshi gida-gida da dama. AT: "Daga iyalin da Yahweh ya zaɓa, kowanne gida za su matso kusa" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-idiom)

Gidan da Yahweh ya ware dole a gabatar da su mutum - mutum

AT: "Daga iyalin da Yahweh ya ware, kowanne mutum zai matso kusa" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-idiom)

duk wanda aka zaɓa

AT: "shi wanda Yahweh ya zaɓa" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

ya karya dokar Yahweh

Karya doka na nufin yin rashin biyayya da shi. AT: Ya yi rashin biyayya da dokar Yahweh" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)