ha_tn/jol/03/12.md

1.3 KiB

Muhimmin Bayani

yahweh ya cigaba da magana da kasashen.

Bari kasashen su tashi kansu ... dukan kasashen da ke kewaye

Kalmomin nan "kasashen" da kuma "kasashen da ke kewaye" na nufin kasashen da ke kewaye da Yahuda. Yahweh zai shar'antasu a gaɓar Yehoshafat domin abinda suka yi wa Yerusalem.

mayar da lauje ... mamatsar inabi ta cika

wasu daga ma'anar maganar nan sune 1) hari akan kasar da ke cike da zunibi na kama da girɓin inabi da kuma matsar ruwarsa, ko kuma 2) hanzarin hukunta kasashen da ke cike da zunubi na kama da hanzarin da ke cikin girbi da kuma matsar inabi.

Lauje

doguwar tankwararrar wuka da ake amfani da ita don girbin hatsi.

girbi ya kosu

"hatsin ya yi daidai na girɓi"

zo, ku matse inabin, gama mamatsar inabin ta cika

Yahweh na kwatanta kasashen da damin inabi a mamatsar inabi, wanda ke shirye domin a matsa. AT: "zo, tattaka kasashen, gama suna kama da inabin da ke cikin mamatsar inabi. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

mataran ta cika har tana zuɓa, gama muguntarsu na da yawa sosai

Yahweh na kwatanta muguntarsu da ruwan inabin da ke gangarowa daga mamatsa zuw mataranta. Mataran bata da girman da za ta dauki yawan mugunta da ke gangarowa a cikinsu. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)