ha_tn/job/36/19.md

1.0 KiB

Ko wadatarka zata amfane ka, domin kada ka shiga damuwa, ko kuwa ƙarfinka zai taimake ka?

Elihu ya yi waɗannan tambayoyin don bayyana cewa kuɗi da iko ba za su iya taimaka wa Ayuba ba idan ya yi rashin gaskiya. AT: "Dukiyarka ba za ta iya sa ka daina kasancewa cikin wahala ba, kuma duk ƙarfin da kake da shi ba zai iya taimaka maka ba." (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

lokacin da a ka kama mutane a cikin wurarensu

Ma'anar mai yiwuwa ita ce 1) cewa "mutane" suna nufin mutane gaba ɗaya kuma "yankewa a wurarensu" wani magana ne na zaluntar wasu ta hanyar fitar da su daga gidajensu. AT: "lokacin da mutane suka jawo wasu daga gidajensu" ko 2) cewa "mutane" wakilci al'ummai ne kuma "yankewa a wurinsu" wani misali ne ga halakar al'umma. AT: "lokacin da al'ummai za su lalace" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Ana gwada ku ta wahala

Ana iya bayyana wannan a cikin tsari mai aiki. AT: "Allah na jarraba ku ta hanyar wahalar da ku" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)