ha_tn/job/31/07.md

944 B

Idan ƙafata ta kauce daga hanya

Anan "mataki na" wani magana ne ga halayen Ayuba, kuma "an bi shi daga madaidaiciyar hanya" magana ne don canji daga rayuwa ta gari. AT: "Idan na canza daga rayuwa ta dama" ko "Idan na daina yin abin da ke daidai" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

idan kuwa zuciyata ta bi sha'awar idanuna

Anan “zuciyata” da “idona” suna game da abin da Ayuba yake so da gani. Zuciyar da ke bin idanu wani kwatanci ne na son aikata abin da ya gani. Yana nuna cewa wannan yana nufin abubuwan zunubi da Ayuba yake gani. AT: "Idan na so yin kowane irin zunubi da na gani" (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-metonymy]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-metaphor]])

to bari na shuka, bari wani yaci, bari kuma amfanina ya tumɓuke

Ayuba yana cewa idan ya yi zunubi da gaske, to wannan mummunan abin da ya kamata ya same shi. Zai yi aiki tuƙuru wajen shuka gonakinsa, amma ba zai iya ci ba.