ha_tn/job/26/13.md

1.7 KiB

Ta wurin numfashinsa yasa sararin sama yayi garau

Wannan hoton yana wakiltar Allah ne yake sa iska ta busa girgije. AT: "Allah ya hura girgije domin sararin sama ya bayyana" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

da hannunsa ya sha zarar macijin nan mai gudu

An ɗauka cewa Allah yana riƙe da takobi, a nan kuma “hannunsa” yana wakiltar wannan takobi. Hakanan, "soke" yana wakiltar kisa. AT: "Da takobinsa ya soki maciji mai gudu" (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-explicit]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-metonymy]])

macijin nan mai gudu

"Macijin kamar yadda yake ƙoƙarin tserewa daga gare shi." Wannan yana nufin Rahab, dodo a cikin teku. Duba Ayuba 26:12.

Duba, amma waɗannan su ne gefuna hanyoyinsa

Anan "gefuna" yana wakiltar karamin sashi wanda zamu iya ganin wani abu wanda yafi girma girma. AT: "Duba, waɗannan abubuwan da Allah ya yi suna nuna kaɗan ne kawai na ikonsa mai ƙarfi" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

yaya ƙanƙantar raɗa da muke ji a gare shi!

Wannan karin magana ce da ke nuna irin mamakin da Ayuba ya yi na duk manyan abubuwan da Allah yayi wanda ba mu san shi ba. Ana ganin abin da Allah yake yi ana maganar jin muryar Allah. AT: "kamar yadda dai mun ji kawai ya rada!" (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-exclamations]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-metaphor]])

Wane ne ya gane tsawar ikonsa?

“Tsawar ikonsa” tana wakiltar girman Allah. Ayuba yayi amfani da wannan tambayar don jaddada cewa ikon Allah yana da girma sosai har ba wanda zai iya fahimtarsa. AT: "Aradu yana nuna girman ikonsa wanda ba wanda zai iya fahimta!" (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-rquestion]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-metaphor]])