ha_tn/job/14/01.md

1.6 KiB

Muhimmin Bayani:

Wannan suran ya ci gaba da jawabin Ayuba, wanda ya fara a cikin Ayuba 12:1. Ayuba yana magana da Yahweh.

Mutum, da mace ta haifa

Wannan yana nufin dukkan mutane, maza da mata; duk an haife su cikin wannan duniya. (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-gendernotations)

ya kan rayu na nan kwanaki

Wannan ƙari ne don ƙarfafawa cewa mutane suna rayuwa ne na ɗan kankanen lokaci. AT: "yana rayuwa na ɗan lokaci kaɗan" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-hyperbole)

na cike da damuwa

Kasancewa "cike da matsala" yana wakiltar fuskantar matsala da yawa. AT: "yana da matsaloli da yawa" ko "yana wahala sosai" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

Ya kan tsiro daga ƙasa kamar fure sai kuma a datse shi

Kamar rayuwar fure, rayuwar mutum takaice kuma tana cikin sauki kashe shi. (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-simile)

kamar inuwa baya daɗewa

Idan aka kwatanta rayuwar mutum da takaitacciyar inuwa wacce take bacewa da sauri. (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-simile)

kana duba kowannensu?

Ayuba ya nuna cewa baya son Allah ya saka masa da hankali sosai. AT: "Ba kwa kallon ɗayan waɗannan." ko "Ba ku mai da hankali sosai ga waɗannan ba. Ina roƙo kar ku mai da hankali gare ni sosai." (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

Duba

Anan, duba na nufin maida hankali akan mutum domin yin masa sharia. AT: "maida hankali" ko "neman laifi a"

Kana gabatar da ni a gaban shari'a tare da kai?

Ayuba yayi wannan tambayar don ya nuna mamakinsa da Allah ke yin masa shari'a duk da cewa shi ba komai ba ne. AT: "Amma kana yin mani sharia" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)