ha_tn/job/13/13.md

886 B

ku kyale ni

Wannan kalma ce da ke nufin "daina damuwa da ni" ko "daina hana ni" wannan na nufin "ku daina damuna" ko "ku daina hanani" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-idiom)

bari abin da zai auko kaina ya auko

Abubuwan da ke zuwa ga mutum suna wakiltar abubuwan da ke faruwa ga mutum. Wannan furcin da ya fara da "bari" yana nufin cewa bai damu da abin da zai iya faruwa da shi ba. AT: "ka bar abin da zai faru da ni ya faru" ko "Ban damu da abin da zai iya faruwa da ni ba" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

zan sa namana a bakina ... a hannuwa na

"Namana" a nan na nufin "rai". "Bakina" da "hannuwa" na nufin cikin ikonsa. Waɗannan kalamai na nunawa Ayuba kasada na ransa domin ya nuna hujjojinsa ga Allah. AT: "Ina shirye in yi kasadar raina" (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-metonymy]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-parallelism]])