ha_tn/job/06/04.md

1.2 KiB

Gama kibawun Mai Iko Dukka suna cikina

Wannan wata kalma don wahalar Ayuba. Ya kwatanta masa dimbin matsalolin sa da kiban da Allah ya buge jikinsa da shi. AT: "Kamar dai Mai Iko Dukka ya harba kibayoyi a cikin jikina" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

razana daga Allah ta shiryo kanta gaba da ni

Ayuba ya yi magana game da mummunan abin da ya same shi kamar dai sojojin da Allah ya shirya su kai masa hari gaba ɗaya. AT: "Allah ya sa dukan mugayen abubuwa da suke faruwa su faru da ni gaba ɗaya" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-personification)

jakin jeji kan yi hargowa idan yana da ciyawa? să kan yi kuka da ciyawa a gabansa?

Ayuba ya gabatar waɗannan tambayoyi na magana don ya nanata cewa yana da dalilin yin gunaguni. Waɗannan tambayoyi ana iya rubuta su azaman kalamai. AT: "Kamar yadda jakin daji ba ya hargowa idan akwai ciyawa, kuma kamar yadda sa ba ya ƙoshin yunwar idan yana da abinci, ba zan yi gunaguni ba ni da dalili" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

Za a iya cin abincin da bashi da ɗanɗano

Za a iya faɗin wannan a matsayin aikatau. AT: "Zaka iya cin abin da bashi da ɗanɗano" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)