ha_tn/job/03/04.md

1.3 KiB

Muhimmin Bayani:

Kalmomin a cikin waɗannan ayoyin suna fatan cewa ranar hahuwar Ayuba ba za ta ƙara kasancewa ba. Wannan na iya nuna cewa ranar, ko da yake a baya, har yanzu ta kasance ko ta yaya.

Bari ranar ta zama baƙa ... kada ma rana ta yi haske a kanta

Waɗannan kalmomin guda biyu sun bayyana duhun ranar da aka haifi Ayuba, don haka yana maimaita nadamar Ayuba da aka haifi shi. (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-parallelism)

Dãma duhu da inuwar kwarin mutuwa ya maishe shi tasu

A nan an yi duhu da inuwa mutuwa kamar dai su mutane ne da za su iya iƙirarin wani abu nasu. Kalmar ''ita'' na nufin ranar haihuwar Ayuba. (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-personification)

Dãma girgije ya tsaya a kanta

Anan ana magana girgije kamar dai mutum ne wanda zai iya rayuwa bisa ranar haihuwar Ayuba. AT: ''Dãma girgije ya rufe shi don kada wani ya gan shi'' (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

dukan abubuwa da suka sa ranar duhu

Wannan na nufin abubuwan da ke toshe hasken rana ne da haifar da duhu. Anan ''baki'' na wakiltar duhu. (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

bata tsoro

''tsorata wannan ranar.'' An yi maganar wannan ranar kamar wani mutum wanda zai iya ba shi tsoro da duhu. (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-personification)