ha_tn/job/01/04.md

1.3 KiB

Aduk kowace keɓeɓeyar rana na kowani ɗa, sai ya ba da

Kalmar ''rana'' wataƙila na nufin ranar da suka yi bikin ranar haihuwar ɗa. Amma aƙalla yana nuni cewa dukan yayansa maza kan dauki wata rana domin yin liyafa. AT: ''A kowace ranar haihuwar ɗa, ɗa zai ba da'' ko ''Kowane ɗa kuma shi zai ba''

Sukan aika a kira ... Ayuba ya aika ... ya tsarkake su ... Ya kan tashi da sassafe ya mika ... ya kan ce

"Suna zama bisa al'ada kuma sun aika ... Ayuba ya saba ke ... ya saba tsarkakewa ... ya saba tun da sassafe ya miƙa ... yana al'ada yace''

tare da su

Kalmar ''su'' na nufin 'ya'ya maza bakwai da 'yan mata uku amma ba su hada da Ayuba ba.

Sa'ad da kwanakin liyafar suka ƙare

''Lokacin da liyafar suka ƙare'' ko ''Bayan liyafar''

Ayuba kan aika su zo

''Ayuba ya aiki wani ya kira su zo wurinsa''

ya kan tsarkake su

A nan ''tsarkakewa'' na nufin a roƙon Allah ya dauke dukkan wani rashin tsarki da 'ya'yan Ayuba suka jawowa kansu yayin da suke farin ciki tare. Ayuba ya yi wannan ta wurin hadaya ga Allah a kansu.

Saɓon Yahweh a cikin zukatansu

''Zukatansu'' na nufin tunaninsu. Sau da yawa irin wannan tunanin kan zo ba zato, ba da son mai yinta ba. AT: ''ya la'ance Allah a cikin tunaninsu'' (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)