ha_tn/jhn/19/01.md

695 B

Mahaɗin Zance:

An cigaba da sashin labarin daga Aya da ta wuce. Yesu ya na tsaye a gaban Bilatus a yayin da Yahudawa suke zargin shi.

Sai Bilatus yayi wa Yesu bulala

Bilatus bai duke Yesu da kansa ba. Anan "Bilatus" magana ne na sojojin da Bilatus ya umurta su duki Yesu. AT: "Sai Bilatus ya sa sojoin su duke Yesu" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-synecdoche)

Ranka ya daɗe, sarkin Yahudawa

A nan amfani da gaisuwan "ranka ya daɗe" da hanu a sama a gaishe da Caesar ne kadai. A yayin da sojojin su na amfani da kayoyi da kaya irin na sarauta su na yi wa Yesu ba'a, da mamaki ne cewa ba su gane wai a hakika shi sarki ne ba. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-irony)