ha_tn/jhn/16/19.md

910 B

Wato kuna tambayar juna ne abinda nake nufi da cewa, ... gan ni'?

Yesu ya yi amfani da wannan tambaya domin almajiransa su yi binbini da abin da ya gaya masu, domin ya iya fasara a gaba. AT: "Ku na tambayan junanku abin da ina nufi loƙacin da na ce, ... gan ni." (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

Hakika, hakika, ina gaya maku

Fasara wannan a yadda harshenku na nanata cewa abin da yake bi ya na da muhiminci kuma gaskiya ne. Dubi yadda kun fasara wannan a cikin 1:51.

amma duniya za ta yi farin ciki

A nan "duniya" magana ne wa mutane da suke hamayya da Yesu. AT: "amma mutane da suke hamayya da Yesu za su yi farin ciki" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

amma bakin cikinku zai koma farin ciki

AT: "amma bakin cikinku zai zama murna" ko "amma daga baya a maimakon yin bakin ciki za ku yi murna sosai" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)