ha_tn/jhn/10/34.md

1.4 KiB

A rubuce yake ... alloli"'?

Wannan magana ya bayyana kamar tambaya ne domin karin bayani. AT: "Ya kamata kun san cewa a rubuce ya ke a shari'ar ku cewa, 'ku alloli ne." (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

ku alloli ne

Yesu a nan ya yi magana daga nassi inda Allah ya kira masubinsa "alloli," watakila domin ya zabe su ne su wakilce shi a duniya.

maganar Allah ta zo

Yesu ya yi maganar sakon Allah kamar mutum ne wanda ya maso kusa da wadanda sun ji shi. AT: "Allah ya faɗi sakonsa" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

ba za a iya karya nassi ba

AT: 1) "ba bu wani da zai iya canza nassi" ko kuma 2) "a ko yaushe nassi yakan kasance gaskiya."

kuna gaya wa wanda Uban ya kebe ya kuma aiko cikin duniya, 'Kana sabo', domin Na ce, 'Ni dan Allah ne'?

Yesu ya yi amfani da wannan tambaya don ya tsawata abokan gabansa domin sun ce ya na sabo a loƙacin da ya kira kansa "Ɗan Allah." AT: "kada ku ce wa wanda Allah ya kebe don ya aika cikin duniya, 'kana sabo; a loƙacin da na ce ni ne Ɗan Allah!" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

Kana sabo

"ka na zagin Allah." Abokan gaban Yesu sun gane cewa a loƙacin da an ce shi ne Ɗan Allah, ya na nufin cewa shi daidai ne da Allah.

Uba ... Dan Allah

Wadannan muhimmin lakabi ne da ya na kwatanta dangantaka a sakanin Allah da Yesu.(Dubi: rc://*/ta/man/translate/guidelines-sonofgodprinciples)