ha_tn/jhn/06/54.md

972 B

Dukan wanda ya ci nama na ya kuma sha jinina yana da rai Madawwami

Su jumlan "ci nama" da " sha jinina" karin magana ne. Kamar yadda wani ya na son abinci da ruwa domin ya samu rai, waddanda sun gaskanta da Yesu za su samu rai na ruhaniya. AT: "Duk wanda ya gaskanta da ni don abincin ruhaniyarsu da kuma ruwa za su samu rai na har abada" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

a ranar karshe

"a ranar da Allah zai hukunta kowa"

namana abinci ne na gaske ... jinina kuma abin sha ne na gaskiya

Kalmomin "abinci ne na gaske" da kuma "sha ne na gaskiya" maganganu ne da yake nufin cewa Yesu ya tanada abincin ruhaniya da ruwan sha wa waddanda sun gaskanta da shi. Karban Yesu a bangaskiya ya na tanada rai na har abada kamar yadda abinci da ruwan sha ya ke amfana jiki. AT: "Ni ce abincin ruhaniya ta gaskiya da kuma ruwan sha" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

zamne a ciki na, ni kuma a cikinsa

"na da dangantaka na kusa da ni"