ha_tn/jer/48/26.md

1.1 KiB
Raw Permalink Blame History

Ka sa ya bugu

Anan ana magana akan mutanen da suke fuskantar horon Yahweh kamar suna shan giya ne, suna yin wauta don mutane suyi musu dariya. AT: "Zan sa ku zama kamar mashayi" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Bari Mowab ta yi birgima a kan hararwarta, ka sa ta zama abin ba a

Yahweh ya ci gaba da magana game da mutanen Mowab kamar su mashayi. AT: "Yanzu mutanen Mowab za su zama kamar mutumin da yake birgima a cikin amai ... abin ba'a (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Domin ko Isra'ila bata zama abin dariya a gare ku ba?

Yahweh yayi amfani da tambaya don tunatar da mutanen Mowab yadda suka yi da mutanen Israila. AT: "Kun kasance kuna yi wa Isra'ilawa dariya da dariya." (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

An same shi cikin ɓarayi, saboda haka ku ka kaɗa kanku gare shi ku ka yi kuma ta yin magana a kansa?

Anan Yahweh yayi amfani da tambaya don tsawata wa mutanen Mowab saboda yadda suka kunyata da Isra'ilawa duk da cewa basu yi wani laifi ba. AT: "Duk da cewa su ba barayi bane, amma har yanzu kun girgiza kan ku ... game dashi." (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)