ha_tn/jer/25/05.md

796 B

Bari kowanne mutum ya juyo daga hanyar muguntarsa da lalatattun ayyukansa

Irmiya yayi magana akan mutanen da suka daina yin wani abu kamar dai waɗancan mutanen suna juya baya ga wannan aikin. (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-doublet)

kuma kada ku cakune shi da ayyukan hannuwanku domin kada ya azabtar da ku

Kalmar "shi" tana nufin Yahweh. Mai yiwuwa ma'anoni ga kalmar "aikin hannuwanku" su ne 1) ishara ce ga gumakan da mutane suka yi da hannayensu. AT: "kada ku tsokane Yahweh da gumakan da kuka yi" ko kuma 2) Kalmomin magana ne da ke nuni ga ayyukan mutum, tare da kalmar "hannaye" kasancewa synecdoche wanda ke wakiltar mutumin da ya aikata waɗannan ayyukan. AT: "kada ku tsokane Yahweh ta hanyar abin da kuke aikatawa" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-synecdoche)