ha_tn/jer/20/07.md

1.2 KiB

Na zama abin dariya dukkan yini, kowa yana ta yi mani ba'a

Waɗannan jimlolin guda biyu ma'anar abu ɗaya ne kuma suna jaddada yadda wasu suke yi masa ba'a. (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-parallelism)

Sai maganar Yahweh ta zama abin zargi da abin ba'a a dukkan yini

Anan "kalma" tana nufin sakon Yahweh. Za a iya fassara kalmomin "zargi" da "izgili" tare da jimloli na magana. AT: "mutane suna zagina da izgili gare ni a kowace rana saboda na yi shelar saƙon Yahweh" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

Ba kuwa zan ƙara yin magana da sunansa ba

Mai yiwuwa ma'anar su ne 1) "Ba zan taɓa ambaton Yahweh ba ko faɗin wani abu game da shi" ko 2) kalmar "suna" tana wakiltar iko. AT: "Ba zan ƙara yin magana a matsayin manzonsa ba" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

Sai in ji kamar wuta a cikin zuciyata, an sa ta a cikin ƙasusuwana

A nan kalmomin "zuciya" da "ƙasusuwa" suna wakiltar ainihin cikin Irmiya. Irmiya yayi maganar rashin iya magana game da sakon Yahweh kamar sakon Yahweh wuta ce da take ci a cikin sa. AT: "Maganar Yahweh kamar wuta ce da take ci a ciki na sosai" (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-metaphor]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-synecdoche]])