ha_tn/jer/13/22.md

1.1 KiB

Mutanen Kush zasu iya sake launin fatarsu

Ana amfani da wannan tambayar ne don bayyana misalin wani abu da ba zai yiwu ba. Ana iya rubuta wannan tambayar azaman sanarwa. Hakanan, kalmar da aka fahimta "iya" ana iya samarda ita a cikin magana ta biyu. AT: "Mutanen Kush ba za su iya canza launin fatar su ba kuma damisa ba za ta iya sauya tabon ta ba." (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

Idan haka ne, to ku kanku, duk da dai kun saba da yin mugunta, zaku iya yin nagarta

Wannan bayanin abin ban dariya ne saboda misalai game da Kushiyawa da damisa yanayi ne da ba zai yiwu ba. Wannan yana nuna cewa idan waɗancan abubuwan da basu yiwu ba zasu iya faruwa to zasu iya yin kyau. AT: "Kamar yadda waɗannan abubuwan basa yiwuwa, haka kuma ba zai yuwu ba a gare ku da kuke aikata mugunta koyaushe ku aikata alheri" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-irony)

zan watsar da su kamar ƙaiƙayi da kan lalace a iskar hamada

"Zan watsar da su kamar ƙaiƙayi wanda iska ke kaɗawa." Yahweh yana cewa zai warwatsa mutanensa a ko'ina cikin duniya kamar yadda iska ke watsuwa. (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-simile)