ha_tn/jer/05/14.md

1.3 KiB

duba zansa maganata cikin bakinka. Zata zama kamar wuta

Anan “sanya maganata a bakinku” yana wakiltar sa Irmiya ya yi maganar saƙon Allah. AT: "Zan sa ku faɗi sakona" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Gama zata cinyesu

"Domin sakona zai cinye su." Sakon Yahweh game da yadda zai hukunta mutanensa, saboda haka yana magana kamar saƙonsa zai hallaka su kamar yadda wuta take lalata itace. AT: "Gama lokacin da kuka faɗi sakona, zai hallaka mutanen Isra'ila kamar yadda wuta ke lalata itace" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

al'ummace wadda ta wanzu, kuma daɗaɗɗiyar al'umma!

Waɗannan jimlolin suna nufin abu ɗaya kuma suna jaddada tsawon lokacin da ƙasar ta kasance. Wannan yana magana ne game da al'ummar da Yahweh zai kawo wa Isra'ilawa daga nesa. AT: "tsohuwar al'umma ce kuma mai dawwama" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-doublet)

Al'umma ce wadda baka san yaren su ba, ba kuwa zaka fahimci abin da suke faɗi ba

Waɗannan jimlolin suna nufin abu ɗaya kuma suna ƙarfafa cewa Isra'ilawa ba su san yaren waɗannan mutanen ba. Yana iya nufin cewa Isra'ilawa ba su da dangantaka da su sosai. AT: "Al'umma ce wacce ba zaku iya fahimtar yarenta kwata-kwata ba" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-parallelism)