ha_tn/jer/02/26.md

1.0 KiB

yake jin kunya idan an kama shi

Wannan karin magana yana nufin wani ya gano cewa abin da mutumin ya yi. Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "lokacin da wani ya same shi" ko "lokacin da mutane suka san cewa ya saci abubuwa" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-idiom)

Waɗannan su suke cewa itace, 'Kai ubana ne,' ga dutse kuma, 'Kai ka haife ni

Anan "itace" da "dutse" suna wakiltar gumakan da aka sassaka daga itace da dutse. Waɗannan kalmomin suna ƙarfafa cewa gunkin an yi shi da abubuwa na yau da kullun kuma bai cancanci a bauta masa ba. AT: "Waɗannan mutane su ne waɗanda suke ce wa katako, "Kai ne mahaifina," da kuma ga dutse da aka sassaka, "Kai haife ni." (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-synecdoche)

Gama bayansu ke fuskanta ta ba fuskokinsu ba

"Bayayyakinsu suna wajena; fuskokinsu ba sa wurina." Wannan yana nuna musu suna kin Allah. AT: "sun juya daga wurina" ť ko "sun juya mini baya ba fuskokinsu ba" ko "sun ƙi ni gaba ɗaya" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)