ha_tn/jer/02/18.md

822 B

Yanzu fa, me ya kai ku hanyar Masar kuka kuma sha ruwayen Shihor? Don me kuka bi hanyar zuwa Asiriya kuma kuka sha ruwayen kogin Yufiratis?

Yahweh yana amfani da waɗannan tambayoyin don tunatar da mutanensa cewa babu wani amfani da zai roƙi Masar da Asiriya su taimake su. AT: "Ba zai taimake ka ba ka je Masar ka sha daga ruwan Kogin Shihor, ko ka je Asiriya ka sha daga ruwan Kogin Yufiretis." (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-metaphor]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-rquestion]])

Muguntarku ta tsauta maku, rashin bangaskiyarku kuma ya hore ku

Duk waɗannan jimlolin suna nufin cewa hukuncinsu sakamakon mummunan halayensu ne. AT: "Saboda kun kasance mugaye kuma marasa aminci, zan hore ku" (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-personification]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-parallelism]])