ha_tn/jdg/02/11.md

1.0 KiB

mugun abu a fuskar Yahweh

"A fuskar Yahweh" a nan na nufin tunanin Yahweh game da abu. AT: "Abun da Yahweh ya ce mugunta ne" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

Ba'aloli

Ana amfani da sunan "Ba'al" wa wani allahn ƙarya, amma ana amfani da kalmar wa dukka allolin da ake bauta musu tare da Ba'al. (Duba: rc://*/ta/man/translate/translate-names)

Sun kauce daga Yahweh

Ana maganar yadda Isra'ilawa sun daina yi wa Yahweh biyyaya kamar suna tare ne sai suka tafi. (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Sun bi waɗansu alloli

Ana maganar yadda Isra'ilawa su ka fara bauta wa allolin ƙarya, kamar Isra'ilawan na tafiya ne da kafafun su, su na kuma bin allolin ƙarya. (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

rusuna ƙasa gare su

Wannan sujada ne da kuma ba wani girma. (Duba: rc://*/ta/man/translate/translate-symaction)

Su ka sa Yahweh ya fusata

"Su ka sa Yahweh ya yi fushi"

Ashtoret

Wannan wata allah ce da ake bauta wa a hanyoyi dabam dabam. (Duba: rc://*/ta/man/translate/translate-names)