ha_tn/jas/05/19.md

1.5 KiB

'yan'uwa

Wannan kalma anan zai iya nufin maza da kuma mata. AT: "'yan'uwanmu masu bi" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-gendernotations)

idan wanin ku ya baude wa gaskiya, wani kuma ya dawo da shi

Anyi magana game da mai bi da ya bar dogara da kuma yiwa Allah biyayya kamar yanda tumaki kan bace daga cikin garke. Ana kuma yi magana game da mutum da ya lallashe shi kamar makiyayi da ya je neman tumakin da ya bace. AT: "duk lokacin da wani ya bar yiwa Allah biyayya, kuma wani mutum ya taimake shi ya cigaba da yin biyayyan kuma" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

duk wanda ya dawo da mai zunubi a hanya daga baudewar sa, .... zai rufe dunbin zunubai

Yakubu na nufin Allah zai more kuzarin mutum mai zunubin ya tuba ya kuma tsira. Amma Yakubu yayi magana kamar wani mutun daban da ya ceci ran mai zunubin daga mutuwa. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

zai cece shi daga mutuwa, kuma zai rufe dunbin zunubai

Anan "mutuwa" na nufin mutuwa na ruhaniya, rabuwa da Allah na har'abada. AT: "zai cece shi daga mutuwan na ruhaniya, kuma Allah zai yafe wa mai zunubin dukan zunuban sa" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-synecdoche)

zai rufe dunbin zunubai

AT: 1) mutumin da ya dawo da ɗan'uwa mara biyayya, za'a yafe masa zunubansa ko 2) ɗan'uwa mara biyayya, in ya koma ga Ubangiji, zai yafe zunuban sa. Anyi maganar zunubi kamar wani abu da Allah ya rufe da ba zai gansu ba, domin ya yafe masu. (See: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)