ha_tn/jas/02/01.md

1.4 KiB

Mahaddin Zance:

Yakubu ya cigaba da gaya was Yahudawa masubi da suke a warwase yanda zasu yi zaman kaunan juna kuma ya tunashe su akan kada su so masu arziki fiye da 'yan'uwa matalauta.

Ku 'yan'uwana

Yakubu yayi la'akari da masu sauraronsa wanda su Yahudawa ne masubi AT: "Yan'uwanmu masubi" ko "'Yan'uwanmu maza da mata a cikin Almasihu"

rike da bangaskiyar ku ga Ubangijinmu Yesu Almasihu

Anyi maganar yarda da Yesu Almasihu kamar wani abu da mutun zai iya rike wa. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Ubangijinmu Yesu Almasihu

Kalmar nan "mu" ya haɗa da Yakubu da sauran 'yan'uwa masubi. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-inclusive)

nuna bambanci ga wadansu mutane

son taimakawa waɗan su mutane fiye da sauran

Idan wani mutum

Yakubu ya fara siffanta yanayin da masubi sun fara daraja masu arziki fiye da matalauta. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-hypo)

da zobban zinariya da tufafi masu kyau

"ya yi ado kamar mai arziki"

ka zauna a nan wuri mai kyau

zauna a wuri mafi girma

ka tsaya daga can

tafi wuri mafi kaskanci

Zauna a nan kasa a gaba na

tafi wuri mafi muhimmanci

ashe ba kuna zartar da hukunci a tsakanin ku ba ke nan? Ba kun zama alkalai na mugayen tunani kenan ba?

Yakubu na morar tambayoyi da ba su damu da amsa ba domin ya koyar ya kuma yi wa masu karantawa tsawa. AT: "kuna hukunci a sakanin ku kuma kuna zama alkalai na mugayen tunani" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)