ha_tn/isa/51/04.md

1.1 KiB

Gama zan zartar da doka, kuma zan sa hukuncina ya zama haske domin al'umma

Anan adalcin Allah yana wakiltar shari'arsa, kuma haske yana wakiltar sanin abin da ke daidai. Wannan yana nufin mutanen al'ummomi zasu fahimta kuma suyi biyayya da dokar Allah. AT: "dokina zai koya wa al'ummai abin da yake daidai" ko "al'ummomi za su san dokokina" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Adalci na ya kusato

Tunanin "kusa" yana wakiltar "ba da daɗewa ba." Adalcin Allah kusa yana wakiltarsa ba da daɗewa ba yana nuna adalcinsa. Zai yi haka ne ta hanyar cika alkawuransa da ceton mutane. AT: "Nan ba da jimawa ba zan nuna adalcina" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

ceto na zai fito

Allah yayi maganar ceton mutane kamar ceton sa abu ne wanda zai iya zuwa gare su. AT: "Zan ceci mutane" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

hannu na zai hukunta al'ummai

Anan hannun Allah yana wakiltar ikonsa, kuma hukunci yana wakiltar mulki. AT: "Zan mallaki al'umman duniya da ƙarfina" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)