ha_tn/isa/50/02.md

1.4 KiB

Me yasa na zo amma babu kowa a wurin? Me yasa na yi kira amma babu wanda ya amsa?

Waɗannan jimlolin guda biyu suna nufin abu ɗaya daidai. Yahweh yana amfani da tambayoyi don ya nanata cewa mutane suna gudun hijira saboda ba su amsa masa ba, ba don ba ya son ya cece su ba. AT: "Lokacin da na zo wurinku, ya kamata ku kasance can, amma ba kwa kasance. Lokacin da na kira ku, ya kamata ku amsa, amma ba ku amsa ba." ko "Lokacin da na zo in yi magana da kai, ba ku amsa mini ba." (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-parallelism]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-rquestion]])

Hannu na ya gajarce ga fansar ku ne? Ko babu iko a gare ni da zan ƙuɓutar da ku?

Yahweh yayi amfani da tambayoyi iri biyu don ya tsawata wa mutane don sun gaskata cewa bai isa ya cece su ba. AT: "Tabbas hannuna bai yi gajarta ba da zan fanshe ku, kuma ina da ikon cetonku!" ko "Lallai ina da ikon kubutar da ku daga abokan gabanku." (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-parallelism]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-rquestion]])

Na suturtar da sararin sama da duhu; Na rufe shi da tsummoki

Waɗannan jimlolin biyu suna nufin abu ɗaya daidai. Yahweh yayi magana akan sanya sama tayi duhu kamar yana sanye da tsummoki. AT: "Ina sanya sama duhu, kamar tana sanye da tsummoki a cikin tsummoki" (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-metaphor]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-parallelism]])