ha_tn/isa/43/08.md

934 B

Wane ne a cikinsu za ya furta wannan, ya kuma yi mana shelar al'amuran farko?

Wannan tambayar ta lafazi ta shafi gumakan da mutanen ƙasashe ke bauta wa. Amsar da aka bayar ita ce babu ɗayansu da zai iya wannan. Ana iya fassara wannan tambayar azaman sanarwa. AT: "Babu wani allahnsu da zai iya bayyana wannan ko ya sanar da mu abubuwan da suka gabata." (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-explicit]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-rquestion]])

Bari su kawo shaidunsu su tabbatar da gaskiyarsu, bari su saurara su kuma tabbatar, 'Gaskiya ne.'

Yahweh yana ƙalubalantar gumakan da al'ummai suke bauta wa don samar da shaidu waɗanda za su ba da shaidar cewa sun sami damar yin waɗannan abubuwa, kodayake ya san cewa ba za su iya yin hakan ba. AT: "Waɗannan alloli ba su da shaidu da za su tabbatar da gaskiyarsu, shaidun da za su saurara kuma su tabbatar, 'Gaskiya ne'" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-irony)