ha_tn/isa/36/18.md

1.0 KiB

Muhimmin Bayani:

Babban kwamandan ya ci gaba da magana da saƙon Sarkin Asiriya ga mutanen Yahuda (Ishaya 36:16).

hannun sarkin Asiriya

An ambaci ikon sarki a matsayin "hannunsa." AT: "ikon sarki" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

Ina allolin Hamat da na Arfad? Ina allolin Sefarwayim? Sun ceci Samariya daga ikona?

Babban kwamandan ya yi amfani da waɗannan tambayoyin don ya yi wa mutanen Yahuda ba'a. Waɗannan tambayoyin na iya haɗuwa kuma a rubuta su azaman sanarwa. AT: "Gumakan Hamat, da Arfad, da Sefarwayim, da na Samariya ba su ceci mutanensu daga hannuna ba." (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

akwai wani da ya ceci ƙasarsa daga ikona, ya ya kuke ganin kamar Yahweh zai ceci Yerusalem daga ikona?

Babban kwamandan ya yi amfani da wannan tambaya don ya yi wa mutanen Yahuda ba'a. Ana iya rubuta wannan tambayar azaman sanarwa. AT: "babu wani allah wanda ya cece ... kuma Yahweh ba zai cece ku a Yerusalem daga ƙarfina ba." (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)