ha_tn/isa/36/11.md

1.1 KiB

Ka yi magana da barorinka

Eliyakim, da Shebnah, da Yowa sun nuna kansu a matsayin shugabannin barorin. Wannan hanyar ladabi ce don magana da wanda ya sami iko sosai.

a kunnuwan mutane waɗanda suke a kan garu

Kalmomin "magana a kunnen wani" na nufin yin magana a inda zasu ji ku. AT: "inda mutanen da suke kan bango za su ji mu" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-idiom)

Babban sarki ya aiko ni ga shugabanku kuma ya faɗi waɗannan maganganu?

Babban kwamandan ya yi amfani da wannan tambaya don ya nanata cewa saƙonsa na dukan mutanen Yahuza ne. Ana iya rubuta wannan tambayar azaman sanarwa. AT: "Tabbas, maigidana ya aiko ni don in yi magana da wannan sakon zuwa gare ku da kuma duk wanda zai iya ji." (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

waɗanda za su ci kashinsu su kuma sha fitsarinsu tare da ku ba?'

Babban kwamandan yayi amfani da wannan tambayar don jaddada cin mutuncin sa. Ana iya rubuta wannan azaman bayani. AT: "Maigidana ya aike ni ga duk wanda ya ji wannan, wanda zai iya ... ku." (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)