ha_tn/isa/33/10.md

1.2 KiB

Yanzu ne za a ɗagani sama; yanzu za a fifita ni

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. Waɗannan jimlolin guda biyu suna da ma'ana iri ɗaya kuma suna nanata cewa ana ɗaukaka Yahweh. AT: "yanzu zan daukaka kaina kuma na nuna cewa na cancanci kowa ya girmama ni" (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-activepassive]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-parallelism]])

Kun ɗauki cikin ƙai-ƙai, kun haifi ciyawa

Wannan yana maganar Asiriyawa suna yin shiri kamar suna daukar ciki kuma suna haihuwar shirinsu kamar yadda uwa take haihuwar jariri. Wannan yana magana ne game da shiryeshiryensu marasa amfani ta hanyar kwatanta su da ƙaiƙayi. AT: "Kuna yin shiryeshiryen da ba su da amfani kamar ƙaiƙayi da ciyawa" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Mutanen za a ƙona su su zama danƙo, kamar yadda a ke sassare sarƙaƙƙiya a ƙone ta

Wannan yana kwatanta yadda mutane za a kone gawawwakin kamar yadda ake kona ƙaya. Haka nan, ana iya bayyana wannan a cikin sigar aiki. AT: "Wuta za ta ƙone mutane gawarwakin zuwa lemun tsami kamar yadda manomi yana sare ƙaya kuma ya ƙone su "(Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-simile]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-activepassive]])