ha_tn/isa/33/07.md

1.0 KiB
Raw Permalink Blame History

jakadun masu begen salama, suna kuka mai zafi

Wannan yana nufin suna kuka saboda ba su yi nasarar yin sulhu ba. AT: "jami'an diflomasiyyar suna fatan zaman lafiya amma ba su yi nasara ba don haka suke kuka mai zafi" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

An yasar da karabku; ba bu sauran matafiya

Dukkanin jumlolin suna jaddada cewa babu matafiya akan manyan hanyoyi. Wadannan za a iya hade su kuma a bayyana su cikin tsari. AT: "Mutane ba su yin tafiya a kan manyan hanyoyi" (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-parallelism]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-activepassive]])

Ana ta tada alƙawari, an wofintar da shaidu, kuma ba nuna bangirma ga ɗan adam

Wannan nassi na iya nufin ishara ga yanayin lalacewar Israila, ko kuma tana iya nufin kasawar alummar ta kulla yarjejeniyoyin zaman lafiya da Asiriya. Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "Mutane suna karya alkawarin da suka yi, mutane suna watsi da shaidar shaidu, kuma mutane ba sa girmama juna" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)