ha_tn/isa/31/05.md

687 B

Kamar tsuntsaye masu shawagi bisa sheƙarsu, haka Yahweh mai runduna zai tsare Yerusalem

A nan an kwatanta yadda Yahweh yake kāre Yerusalem da yadda uwa tsuntsu take kāre tsuntsaye jariransu a cikin gidansu. (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-simile)

zai tsare ya kuma cece ta sa'ad da ya ke wuce wa bisanta ya kare ta

Wannan yana magana ne akan yadda Yahweh yake kiyayewa da tseratar da Yerusalem, yana mai bayyana shi a matsayin tsuntsayen da ke shawagi akan garin. AT: "zai kare da kuma ceton garin daga abokan gaba" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Ki komo wurinsa shi wanda kika juya nesa daga gare shi

"Ku koma zuwa ga wanda kuka yi wa tawaye"