ha_tn/isa/29/15.md

610 B

waɗanda suke ɓoye wa Yahweh shirye-shiryensu

Mutanen da suke ƙoƙarin yin shiri ba tare da Yahweh sun sani ba ana maganarsu kamar suna ɓoye shirye-shiryensu a cikin wani wuri mai zurfi inda Yahweh baya iya gani. AT: "waɗanda suke ƙoƙarin ɓoye shirinsu daga Yahweh" ko "waɗanda suke ƙoƙarin hana Yahweh gano abin da suke shirin yi" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

waɗanda ayyukansu suke cikin duhu

Ana nuna cewa suna aikata mugunta a ɓoye. AT: "waɗanda ke aikata mugunta a cikin duhu don haka ba wanda zai iya ganin su" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)