ha_tn/isa/29/09.md

1.3 KiB

Ku jiwa kanku mamaki, ku kuma yi mamaki

Kalmar "kanku" tana nufin mutanen Yerusalem. Dalilin da yasa suke mamakin za'a iya bayyana su a sarari. AT: "Ka yi mamakin abin da zan gaya maka" (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-explicit]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-doublet]])

ku makantar da kanku, ku zama makafi

Mutanen da ba su kula da abin da Yahweh ya faɗa ana maganarsu kamar suna makantar da kansu. AT: "ci gaba da kasancewa jahilai da ruhaniya ga abin da nake nuna muku" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Ku bugu, amma bada ruwan inabi ba, amma bada giya ba

Mutane suna rashin hankali da rashin fahimtar abin da Yahweh yake yi, ana maganarsu kamar suna maye. AT: "Ku zama marasa azanci kamar mashayi, amma ba don kun sha giya da yawa ko giya ba" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Gama Yahweh ya kwararo maku ruhun barci mai nauwi

Anan "ruhun" yana nufin "a sami halayyar" bacci. Ana magana game da Yahweh mai sa mutane suyi bacci kamar "ruhun" wani ruwa ne da ya zubo kan mutane. Hakanan "bacci mai nauyi" kwatanci ne wanda yake nufin mutanen basu da hankali kuma basa iya fahimtar abin da Yahweh yake yi. AT: "Dalilin da yasa ba ku da hankali shi ne saboda Yahweh ya sa ku barci cikin ruhaniya" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)