ha_tn/isa/29/01.md

792 B

Kaiton Ariyel

Anan "Ariyel" yana wakiltar mutanen da suke zaune a cikin garin Ariyel. AT: "Kaiton abin da zai kasance ga mutanen Ariyel" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

birnin da Dauda ya kafa zango

"Dauda ya zauna" ko "Dauda ya rayu"

A ƙara shekara kan shekara; bari bukukuwa su kewayo

"Ku ci gaba da yin bikinku shekara da shekara." Wannan magana ce ta izgili. Yahweh ya gaya wa mutane su ci gaba da yin bukukuwan idinsu a inda suke miƙa masa hadaya, amma ya san hakan ba zai hana shi hallaka su ba. (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-irony)

zata yi ta makoki da kururuwa

Kalmomin "makoki" da "kururuwa" ma'anarsu abu ɗaya ne da kuma jaddada tsananin baƙin ciki. AT: "za su yi baƙin ciki sosai" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-doublet)