ha_tn/isa/28/20.md

933 B

Gama gadon ya gajarce da mutum ya miƙe a bisansa, bargon kuma bashi da fãɗin da zai isa ya rufe kansa

Wataƙila wannan karin magana ne da mutane suka sani a lokacin. Yana nufin cewa abin da suka yi imani zai kiyaye shi daga azabar Yahweh zai ɓata musu rai kamar gado da ya yi gajere sosai ko kuma bargo da ke kunkuntar. (Duba: rc://*/ta/man/translate/writing-proverbs)

Dutsen Ferazim ... Kwarin Gibiyan

Waɗannan suna nufin wuraren da Allah ya ci nasara bisa sojojin abokan gaba ta mu'ujiza. (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-explicit]] da [[rc:///ta/man/translate/translate-names]])

bãƙon aikinsa, ya kuma yi bãƙon aikinsa

Waɗannan jimlolin guda biyu suna nufin abu ɗaya. Wannan aikin baƙon abu ne domin Allah yana amfani da sojojin ƙasashen waje don fatattakar mazaunan Yerusalem maimakon ya taimaki mutanen Yerusalem su fatattaki abokan gaba. (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-doublet)