ha_tn/isa/28/17.md

1005 B

Zan sa gaskiya ta zama sandar gwaji, adalci kuma igiyar awo

Gwajin Yahweh bisa ga adalcinsa da adalcinsa don sanin idan mutane masu adalci ne kuma ana magana da su kamar shi magini ne ta amfani da kayan aiki don ƙaddara cewa wani abu daidai yake daidai kuma dai-dai yake. (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

ta share mafaƙar ƙarairayi

Wannan yana magana ne game da "karya" kamar dai su wurare ne da mutum zai iya zuwa ya buya. Suna wakiltar abin da shugabannin Yerusalem suka dogara da shi don kiyaye su daga azabar Yahweh. Mai yiwuwa ma'anoni su ne 1) shugabanni su amince da ƙarairayin da suka faɗa don kare kansu ko 2) shugabanin sun amince cewa alkawarin da suka yi da gumakan ƙarya na wurin matattu zai kiyaye su ko 3) shugabannin sun aminta da cewa yarjejeniyar da suka kulla tare da Masarawa zai basu kariya. Duba yadda kuka fassara makamancin kalmar a cikin Ishaya 28:15. (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-metaphor]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-explicit]])