ha_tn/isa/23/15.md

892 B

za a manta da Taya har shekara saba'in

Tun da mutane ba za su ƙara zuwa Taya don sayo ko sayar da kaya ba, zai zama kamar sun manta da garin. Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "shekara saba'in zai zama kamar mutane sun manta da Taya" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

kamar kwanakin sarki

"kamar shekarun sarki" ko "wanda yake kusan tsawon ran sarki"

ke karuwar da a ka manta da ita; ki kaɗa su da kyau, ki yi waƙoƙi masu yawa, domin a tuna dake

Wannan yana magana ne game da mutanen Taya kamar suna karuwa (aya 15). Kamar yadda karuwa wacce ba ta da farin jini a yanzu za ta iya raira waƙa a kan tituna don dawo da tsoffin ƙaunatattunta, mutanen Taya za su yi ƙoƙari su sa mutane daga wasu ƙasashe su dawo gare su don ci gaba da kasuwanci don mutanen Taya su zama masu arziki da iko sake. (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)