ha_tn/isa/19/16.md

1.1 KiB

Masarawa za su zama kamar mata

Wannan yana nanata cewa mutanen Masar zasu kasance cikin tsoro da rashin taimako idan Allah ya hukunta su. (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-simile)

saboda ɗagaggen hannun Ubangiji mai runduna a kansu

Anan “hannu” yana nufin ikon Allah, kuma ɗaga hannu a kansu yana wakiltar hukunta su. AT: "saboda Yahweh Mai Runduna ya ɗaga ikonsa mai ƙarfi don azabtar da su" (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-metonymy]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-metaphor]])

Ƙasar Yahuda za ta zama sanadin tangaɗin Masar

“ƙasar Yahuda” da “Masar” suna nuni ga mutanen da ke waɗannan wuraren. Masarawa za su yi tuntuɓe domin suna tsoro. AT: "Mutanen Yahuda za su sa Masarawa su yi tuntuɓe" ko "Mutanen Yahuda za su sa Masarawa su firgita ƙwarai" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

Dukkan sa'ad da wani ya tuna masu da ita, za su ji tsoro

Anan, "su" da "su" suna nufin Masarawa kuma "ita" tana nufin mutanen Yahuda. AT: "Duk lokacin da wani ya tunatar da Masarawa game da mutanen Yahuza, Masarawa za su ji tsoro"