ha_tn/isa/14/12.md

1.1 KiB

Yadda ka faɗo daga sama, tauraron rana, ɗan asubahi

Tauraron rana tauraro ne mai haske wanda yake wayewa kafin wayewar gari. Mutanen Isra'ila za su koma zuwa ga sarkin Babila dangane da wannan tauraruwa don su nuna cewa ya taɓa zama babba, amma yanzu bai kasance ba. AT: "Kun kasance kamar tauraron asuba mai haske, amma kun fado daga sama" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Yadda aka sãre ka ƙasa

Mutanen Isra'ila za su yi magana game da sarkin Babila kamar wanda aka sare shi itace. AT: "An kayar da ku kamar itacen da wani ya sare ƙasa" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

zan zauna bisa tsaunin taruwar jama'a

Wannan yana magana ne game da tatsuniyar da mutane da yawa a Gabas ta Tsakiya suka sani, cewa gumakan Kan'aniyawa sun haɗu a majalissar a kan dutse a arewacin Siriya. Zama a kan dutse yana wakiltar mulki tare da gumakan. AT: "Zan yi mulki a kan dutsen da gumakan suke haduwa" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

cikin ƙarshen arewa

"a mafi yawan wuraren arewa." Da alama an kira dutsen a arewa Zaphon. Wasu sifofin zamani sun ce "can nesa da gefen Zaphon."