ha_tn/isa/14/07.md

1.1 KiB

Dukkan duniya

Wannan yana nufin kowa da kowa a duniya. AT: "kowa da kowa a duniya" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

Har itatuwan sayfres suna murna da kai tare da Sidas na Lebanon

Ishaya yayi maganar bishiyoyi kamar dai mutane waɗanda zasu iya murna. Wannan ya nanata cewa babban abu ne cewa Allah ya dakatar da sarkin Babila wanda har ma ɗabi'a za ta yi farin ciki idan za ta iya. AT: "Zai zama kamar ma idan bishiyoyin cyprus da itacen al'ul na Lebanon sun yi murna a kanku" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-personification)

Lahira daga ƙasa na marmarin saduwa

Ana magana da Lahira kamar mutum ne mai ɗoki ya sadu da baƙinsa. Wannan yana nuna cewa sarki ya mutu. AT: "Lahira kamar mai gida ne mai son saduwa da ku" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-personification)

Ta tayar da mattatu domin ka, dukkan sarakunan duniya

"yana rayar da matattu a gare ku, duk sarakunan duniya." Ana magana da Lahira kamar mutum ne wanda zai iya farka waɗanda suke cikinta. AT: "Duk matattun sarakunan duniya a cikin Lahira suna tashi don gaishe ku" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-personification)