ha_tn/isa/11/03.md

1.6 KiB

ba zaiyi shari'a bisa ga abin da idanunsa suka gani ba

Kalmomin "abin da idanunsa suka gani" yana nufin ganin abubuwan da ba su da mahimmanci don yanke wa mutum hukunci dai-dai. AT: "ba zai hukunta mutum ba kawai ta hanyar ganin yadda mutumin yake kama" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

ba kuwa zai yi hakunci bisa ga abin da kunnensa ya ji ba

"kuma ba zai yanke shawara da abin da kunnuwansa suka ji ba." Kalmomin "abin da kunnuwansa suka ji" yana nufin jin abin da mutane ke faɗi game da wani. AT: "kuma ba zai hukunta mutum ba kawai ta hanyar jin abin da wasu ke faɗi game da shi" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

Zai bugi duniya da sandar bakinsa

Kalmar nan "ƙasa" a nan tana wakiltar mutane a duniya. Bugun su da sandar bakinsa yana wakiltar hukunta su, kuma wannan hukuncin zai kai ga hukunci. AT: "Zai yi hukunci ga mutanen duniya, kuma za a hukunta su" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

Adalci zai zama ɗammarar ƙugunsa

Sanya adalci kamar ɗamara yana wakiltar zama adali. Zai yiwu ma'anoni su ne 1) adalcin sarki zai ba shi damar yin sarauta. AT: "Adalcinsa zai zama kamar ɗamara a kugu" ko 2) adalcin sarki zai nuna ikonsa na yin mulki. AT: "Zai yi mulkin adalci" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

ɗammara kewaye da kwatangwalonsa

Sanya aminci kamar ɗamara yana wakiltar kasancewa da aminci. Zai yiwu ma'anoni su ne 1) amincin sarki zai ba shi damar yin sarauta, ko 2) amincin sarki zai nuna ikonsa na mulki. AT: "amincinsa zai zama kamar ɗamara a ɗamarar sa" ko "zai yi mulki cikin aminci" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)