ha_tn/isa/10/26.md

1.5 KiB

zai tayar da bulala akansu

"zai doke Asiriyawa da bulala." Allah ba zai yi amfani da bulala ba da gaske. Wannan yana nufin ikon Allah na azabtar da Asiriyawa sosai. AT: "zai azabtar da Asiriyawa azaba kamar da bulala" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

kamar yadda ya fatattaki Midiyan a Tsaunin Oreb

Wannan yana nufin lokacin da Allah ya taimaki wani mutum mai suna Gideon ya cinye sojojin Midiyanawa. (Duba: rc://*/ta/man/translate/translate-names)

Zai ɗaga sandarsa bisa teku ya ɗaga ta sama kamar yadda ya yi a Masar

Wannan yana magana ne game da Allah wanda ya ceci mutane daga Assuriyawa kamar su sojojin Masar ne. Wannan yana nufin lokacin da Allah ya sa ruwan Bahar Maliya ya tsage don Isra'ilawa su tsere daga rundunar Masarawa kuma sojojin Masar su nutsar da shi. AT: "Zai taimake ku ku tsere daga sojojin Asiriya kamar yadda ya taimaka wa kakanninku suka tsere daga sojojin Masar" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

nauyin kayansa an ɗauke shi daga kafaɗarki kuma karkiyarsa an ɗauke daga wuyanki

"Yahweh zai ɗaga nauyin da Asiriyawa suka ɗora a wuyanka, zai kuma kawar da karkiyar da suka sa a wuyanku." Waɗannan jimlolin biyu suna nufin abu ɗaya daidai. Kalmomin "nauyi" da "karkiya" na nuni ga bauta. Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "Yahweh zai cire Asiriyawa da suka zalunce ku kuma zai hana su sanya ku bayin su" (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-activepassive]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-parallelism]] da rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)