ha_tn/isa/10/17.md

1.1 KiB

Hasken Isra'ila kuma zai zama wuta

Kalmomin "hasken Isra'ila" na nufin Yahweh. Babu tabbacin ko Yahweh ko Ishaya suna magana. AT: "Ni, Yahweh, hasken Isra'ila, zan zama kamar wuta, mai iya hallaka duk wanda ba ya girmama ni" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Mai Tsarkin nasa kuma harshen wuta

"Ni, Yahweh, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, zan zama kamar harshen wuta." Duba yadda kuka fassara "Mai Tsarki" a cikin Ishaya 1: 4.

za ya ƙone ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya ya cinye su rana ɗaya

"Wuta za ta ƙone ta cinye ƙaya da sarƙar Sarkin Asiriya." Mai maganar yayi kwatancen rundunar sarkin Assuriya da ƙayoyi da sarƙaƙƙiya. Wannan yana nanata yadda Allah zai hallakar dasu cikin sauki. AT: "Zan hallakar da Asiriyawa kamar wuta mai ƙaya da ƙayayuwa" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Yahweh kuma zai cinye darajar kurminsa da gonarsa mai albarka

Zai yiwu ma'anar ita ce 1) "Yahweh zai halakar da manyan gandun daji da gonaki a cikin ƙasar Asiriya" ko 2) "Yahweh zai halakar da sojojin Asiriya kamar yadda wuta ke cin manyan dazuzzuka da gonaki." (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)