ha_tn/isa/10/14.md

1.2 KiB

Hannuna ya tsaya, kamar sheƙa, dukiyar dangogi

Sarkin Asiriya ya kamanta karɓar dukiyar al'ummai da na wanda yake karɓar ƙwai daga sheƙan tsuntsu. Wannan yana jaddada yadda ya kasance mai sauƙi a gare shi da rundunarsa su ci waɗancan masarautun. AT: "Sojoji na sun wawushe dukiyar daga al'ummu kamar yadda mutum ke karbar kwai daga gida" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-simile)

kamar wanda ya tattara ƙwan da aka ƙyale. Na tattaro dukkan duniya.

Sarkin Asiriya yana maganar mamaye al'ummai kamar yana tattara ƙwai. AT: "kamar yadda mutum yake daukar kwai daga gurbi lokacin da tsuntsayen ba ya nan don kare su, haka ma runduna ta ta kwashe dukiyar al'umma" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-simile)

Ba bu wanda ya motsa fiffike, ko ya buɗe baki balle suyi ƙara

Wannan yana kwatanta al'ummomi da tsuntsu wanda ke zaune a hankali yayin da ake ɗaukar ƙwan nata. Wannan ya nanata cewa al'ummu ba su yi komai ba yayin da sojojin Asiriya suka kwashe dukiyoyinsu. AT: "Kuma kamar tsuntsun da ba ya sauti ko ya fuka fukafukinsa lokacin da wani ya saci ƙwai nata, al'ummomi ba su yi komai ba kamar yadda muka ɗauke taskarsu" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-simile)