ha_tn/isa/10/10.md

825 B

Kamar yadda hannuna ya yi nasara

"Hannun" a nan yana nufin ƙarfin soja. AT: "Kamar yadda dakaru masu ƙarfi suka ci nasara" ko "Kamar yadda na ci nasara" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-synecdoche)

kamar yadda na yi da Samariya da gumakanta marasa amfani

Kalmar "Samariya" tana nufin mutanen da suke zaune a wurin, kuma "ta" tana nufin birnin Samariya. Garuruwa da al'ummomi galibi ana maganarsu kamar suna mata. AT: "kamar yadda na yi wa mutanen Samariya da gumaka marasa amfani" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

ba zan yi irin wannan kuma ga Yerusalem da gumakanta ba?

Sarkin Asiriya ya yi amfani da wannan tambayar don ya jaddada tabbacin cewa zai ci mutanen Yerusalem da yaƙi. AT: "Lallai zan yi wa Yerusalem da gumakanta haka!" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)