ha_tn/isa/02/09.md

1.3 KiB

Za a sunkuyar da mutane ƙasa, mutum zai faɗi ƙasa

Anan kasancewa ƙasa ƙasa yana wakiltar mutanen da aka wulakanta su gaba ɗaya saboda sun fahimci duk abin da suka dogara da shi ba shi da amfani, kuma ba za su iya yin komai don taimakon kansu ba. Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "Allah zai kunyata mutane, kuma za su gane cewa duk abin da suka dogara da shi ba shi da amfani" (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-metaphor]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-activepassive]])

Ku je wurare masu duwatsu

Mai yiwuwa ma'anoni su ne mutane su shiga 1) kogwanni a kan tsaunuka masu tsayi ko 2) wuraren da akwai manyan duwatsu da yawa waɗanda za a ɓoye a cikinsu.

ku ɓoye wa hukuncin Yahweh

AT: "don gujewa daga firgitawar Yahweh" ko "daga Yahweh saboda za ku ji tsoron shi ƙwarai" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-abstractnouns)

Za a ƙasƙantar da kallon girman kan mutum

"Yahweh zai saukar da duban mutum." Wani mutum mai "girman ido" yana kallon sama da kowa don ya nuna musu cewa ya fi su. Anan duk mutane sunyi laifi da tunanin sun fi Yahweh kyau, kuma yadda suke kallon waɗanda suke bauta wa Yahweh, alama ce ta girman kansu. AT: "Yahweh zai ba da kunya ga dukkan mutane saboda suna ganin sun fi shi kyau" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)