ha_tn/isa/02/03.md

777 B

don ya koya mana waɗansu hanyoyinsa, mu kuma yi tafiya cikin tafarkunsa

Kalmar "hanyoyi" karin magana ne na yadda mutum yake rayuwa. Idan yarenku yana da kalma ɗaya tak don ƙasar da mutane suke tafiya a kanta, za ku iya haɗa waɗannan jimlolin. AT: "yana iya koya mana nufinsa domin mu yi masa biyayya" (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-parallelism]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-metaphor]])

Gama daga Sihiyona shari'a za ta fito maganar Yahweh kuma daga Yerusalem

Waɗannan jimlolin suna nufin abu ɗaya. Ishaya yana nanata cewa dukkan al'ummai zasu fahimci cewa ana samun gaskiya a Yerusalem. AT: "Mutanen Sihiyona za su koyar da shari'ar Allah, kuma mutanen Yerusalem za su koyar da kalmar Yahweh" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-parallelism)