559 B
559 B
Kamar yadda Shalmanesar ya hallaka Bet-arbel a ranar yaki
Ana kwatanta yakin da ke zuwa da wani yaki da aka yi da dadewa a baya.
Shalmanesar
Wannan sunan sarkin da ya hallaka birnin Bet-arbel a wajejen shekara 740 BC. Mayakansa sun kashe mata da kananan yara a wannan harin.
Bet Arbel
Akwai yiwuwar wannan sunan wani birni ne na kabilar Naftali.
Haka za a yi muku, ya utanen Betel, saboda yawan muguntarku
A nan, "Betel", tana wakiltan mutanen da suke zama a wurin, Annabin ya yi magana da mutanen Betel kamar suna nan a wurin suna sauraronsa.