644 B
644 B
Muhimmin Bayani:
Yahweh yana magana.
Ku shuka wa kanku adalci, ku girbe albarkun alkawarin aminci
Ana maganar adalci da alkawarin aminci kamar hatsi ne da za a iya shukawa a girbe.
Ku yi kaftun saurukanku
Sa'adda ba a yi "kaftun" kasa ba, to, ba ta kai a yi shuka a kanta ba. Yahweh yana nufin cewa yana so jama'ar Isra'ila su tuba, domin su fara yin abin da yake da kyau.
Kun shuka mugunta, kun girbi rashin adalci
Ana mugunta da rashin adalci kamar hatsi ne da za a iya shukawa a girbe.
Kun ci amfanin yaudara
Ana maganar sakamakon yaudara kamar abinci ne da za a iya ci. A.T: "Yanzu kuna fama da sakamakon yaudarar juna".